Jump to content

Sadique Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sadique Abubakar
Chief of the Air Staff (en) Fassara

13 ga Yuli, 2015 - 26 ga Janairu, 2021
Rayuwa
Haihuwa Azare, 8 ga Afirilu, 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a

Air Marshal Sadique Abubakar (an haife shi a ranar 8 ga watan Afrilu, shekara ta 1960) shi ne babban hafsan hafsoshin sojojin sama na Najeriya (NAF). Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin Shugaban hafsan sojojin sama a ranar 13 ga watan Yulin, na shekara ta 2015.[1]

Fage da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Sadique Abubakar an haife shi a Tamar 8 ga watan Afrilu shekara ta 1960 a Azare, dake jahar Bauchi State. kuma yayi makarantar firamare dinshi a nan Bauchi daga 1967 zuwa 1973, sannan yayi makarantar sakandare a nan Government Secondary School, dake Bauchi. Abubakar san nan yashiga Nigerian Air Force a matsyin memba na najeriya Military Trainin dinshi a (CMTC 5) a watan Nuwamba 1979.[2]

Abubakar yana da difloma a cikin Gudanar da Jama'a da kuma digiri na farko na Kimiyya (aji na biyu na sama) a kimiyyar siyasa. Ya kuma yi Digirin sana biyu a fannin ilimin dabaru daga Jami’ar Ibadan . Abubakar yana da Helikofta na lasisin kasuwanci (CPL) Helikofta tare da Kayan aiki kuma ya tashi jimillar nau'ikan jirgin sama 7: Bulldog, Piper Warrior, Enstrom, Bell 206, BO-105, Mi-35P da Mi- 17.[3]

Sauran Nade-naden da Abubakar ya yi a baya sun hada da shugaban tsare-tsare da tantancewa, hedikwatar NAF, shugaban sadarwa da tsaro, kwamandan rundunar NAF. Ya yi aiki a matsayin Shugaban Gudanarwar, Hedikwatan NAF kafin nadin nasa a matsayin shugaban sojojin Sama.[4]

  1. "Buhari appoints new service chiefs, Olonishakin new CDS". The News Nigeria. Retrieved 15 July 2015.
  2. "Chief of Air Staff: Air Vice Marshal SB Abubakar". The Nigerian Airforce. Archived from the original on 25 June 2014. Retrieved 15 July 2015.
  3. "Chief of Air Staff: Air Vice Marshal SB Abubakar". The Nigerian Airforce. Archived from the original on 25 June 2014. Retrieved 15 July 2015.
  4. Ugwuanyi, Sylvester. "Buhari appoints new Service Chiefs". Daily Post Nigeria. Retrieved 15 July 2015.