Sadique Abubakar
Sadique Abubakar | |||
---|---|---|---|
13 ga Yuli, 2015 - 26 ga Janairu, 2021 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Azare, 8 ga Afirilu, 1960 (64 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ibadan | ||
Sana'a |
Air Marshal Sadique Abubakar (an haife shi a ranar 8 ga watan Afrilu, shekara ta 1960) shi ne babban hafsan hafsoshin sojojin sama na Najeriya (NAF). Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin Shugaban hafsan sojojin sama a ranar 13 ga watan Yulin, na shekara ta 2015.[1]
Fage da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Sadique Abubakar an haife shi a Tamar 8 ga watan Afrilu shekara ta 1960 a Azare, dake jahar Bauchi State. kuma yayi makarantar firamare dinshi a nan Bauchi daga 1967 zuwa 1973, sannan yayi makarantar sakandare a nan Government Secondary School, dake Bauchi. Abubakar san nan yashiga Nigerian Air Force a matsyin memba na najeriya Military Trainin dinshi a (CMTC 5) a watan Nuwamba 1979.[2]
Abubakar yana da difloma a cikin Gudanar da Jama'a da kuma digiri na farko na Kimiyya (aji na biyu na sama) a kimiyyar siyasa. Ya kuma yi Digirin sana biyu a fannin ilimin dabaru daga Jami’ar Ibadan . Abubakar yana da Helikofta na lasisin kasuwanci (CPL) Helikofta tare da Kayan aiki kuma ya tashi jimillar nau'ikan jirgin sama 7: Bulldog, Piper Warrior, Enstrom, Bell 206, BO-105, Mi-35P da Mi- 17.[3]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Sauran Nade-naden da Abubakar ya yi a baya sun hada da shugaban tsare-tsare da tantancewa, hedikwatar NAF, shugaban sadarwa da tsaro, kwamandan rundunar NAF. Ya yi aiki a matsayin Shugaban Gudanarwar, Hedikwatan NAF kafin nadin nasa a matsayin shugaban sojojin Sama.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Buhari appoints new service chiefs, Olonishakin new CDS". The News Nigeria. Retrieved 15 July 2015.
- ↑ "Chief of Air Staff: Air Vice Marshal SB Abubakar". The Nigerian Airforce. Archived from the original on 25 June 2014. Retrieved 15 July 2015.
- ↑ "Chief of Air Staff: Air Vice Marshal SB Abubakar". The Nigerian Airforce. Archived from the original on 25 June 2014. Retrieved 15 July 2015.
- ↑ Ugwuanyi, Sylvester. "Buhari appoints new Service Chiefs". Daily Post Nigeria. Retrieved 15 July 2015.