Jump to content

Bacci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bacci
biological process (en) Fassara da state of consciousness (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na multicellular organismal process (en) Fassara da hali
Facet of (en) Fassara Lafiya
Yana haddasa sleeping (en) Fassara
Karatun ta somnology (en) Fassara
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C73425
Hannun riga da wakefulness (en) Fassara
Wasu na Bacci
Iyalan wani gida na Bacci

Bacci wata ni'ima ce daga cikin ni'imomin Allah mai girma da buwaya, wadda yake azurta bayinsa da ita. Domin kowace halitta indai mai rai ce tana bacci, mutane da dabbobi duka. Barci itace kishiyar farke, yayinda yanayin tunani ke sauyawa zuwa yanayi na nutsuwa, kwakwalta ta huta, gabobi da jijiyoyi su kwanta, sannan kuma mu'amala da muhalli ya ragu.[1]

Mage na bacci

Shi kuma bacci ya danganta da yadda mutum ya saba ma kansa, wani zai iya daukar awanni masu yawa yana bacci wani kuma awanni kadan sun ishe shi. Amma dai Likitoci sun yi bayanin iya adadin da mutum yake bukata, misali. Babban mutum yakan bukatu da bacci daga awa bakwai (7) zuwa takwas (8) (7-8hrs) a cikin awa ashirin da hudu (24hrs). Shi kuma yaro daga awa goma (10) zuwa sha biyu (12) (10-12hrs) a cikin (24hrs)

Menene bacci zan iya cewa bacci shi ne tafiyar hankali da tunani da ji da gani da rashin sanin meke gudana a lokacin bacci. A takaice bacci yana nufin hutu. A saboda hakane ma Hausawa ke mashi kirari da bacci kanin mutuwa, kuma haka ne saboda idan mutum yana bacci to bai san wanda yake zuwa da dawo ba. Musamman baccin Yara da wasu daga cikin manya.

yaro Yana bacci
Yanda ake bacci

Bacci anayin shi ta nau'uka daban-daban kowa kuma da kalan nau'in nashi. Sai dai bacci a Musulunci yana da ka'idojin da idan mutum yabi su yakan samu tsari daga shaidanu da aljanu ya kuma samu Lada daga mahaliccinsa. Annabi Muhammad (S A W) ya koyar da mu wasu ladubban bacci ga kadan daga wadanda zan iya kawo wa:

  1. Alwala
  2. Addu'a irin karanta Ayatul Kursiyyu sau daya Falaki da Nasi kafa Uku-uku, in ya gama karanta su sai ya hade hannanyen sa ya tofa sai ya shafe jikin shi duka zai fara daga kai har iya inda kuma hannanyensa ya kai.
  3. doki Yana sharara bacci
    Kwanciya a ta gefen dama (akan hannu dama) hannun mutum a kuncin sa, hannun dama kenan sai na hagu ya dora shi akan jikin shi. A daidai lokacin akwai kuma wata addu'a da ake so mun ya yi (باسمك اللهم أموت وأحيا. اللهم قني عذابك يوم تبعث عبادك) shi kenan sai mutum ya fara baccinsa.
  1. "Brain Basics: Understanding Sleep". National Institute of Neurological Disorders and Stroke.