Jump to content

Marie-Angélique Savané

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marie-Angélique Savané
Rayuwa
Haihuwa Dakar, 2 Nuwamba, 1947 (77 shekaru)
ƙasa Senegal
Ƴan uwa
Abokiyar zama Landing Savané (en) Fassara
Yara
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, sociologist (en) Fassara, Mai kare hakkin mata da ɗan jarida

Marie-Angélique Savané (née Sagna, an haife ta biyu 2 ga watan Nuwamba 1947) ƙwararriyar ilimin zamantakewa ce kuma mai fafutuka akan mata, wacce ta kasance "mai matuƙar goyon bayan gyare-gyaren doka da zamantakewa a cikin al'ummar Senegal a madadin mata", a cewar ƙamus na Tarihin Afirka. . An kira ta daya daga cikin jagaban matan Afirka.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a ranar biyu 2 ga watan Nuwamba a shekara ta 1947 a Dakar, Senegal, cikin dangin Katolika .

Daga 1974 zuwa 1978, Savané ta kasance Babbar Editan Mujallar Famille et Développement (Family and Development), "mujallar taimakon kai da kai a yankin Saharar Afrika". A lokacin da take rike da mukaminta ta mayar da mujallar daga yammacin Afirka zuwa wani ra'ayi na Afirka, akan "taimakawa 'yan Afirka su taimaki kansu". [1]

Savané ta yi aiki ga Majalisar Dinkin Duniya, kuma a matsayin mai ba da shawara ga kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya daban-daban na tsawon shekaru masu yawa.

Savané mai haɗin gwiwa ce ta Ƙungiyar Matan Afirka don Bincike.

Rayuwarta ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi aure da Landing Savane Wanda (an haife shine a shekara ta 1945) ɗan siyasan Senegal na hagu, kuma Sakatare-Janar na And-Jëf / Jam'iyyar Afirka ta Dimokuradiyya da Socialism .

Su ne iyayen ga ƙwararren ɗan wasan ƙwallon kwando Sitapha Savané .

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named auto1