Jump to content

Pontedera

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Pontedera
Wuri
ƘasaItaliya
Region of Italy (en) FassaraTuscany (en) Fassara
Province of Italy (en) FassaraProvince of Pisa (en) Fassara
Commune of Italy (en) FassaraPontedera (en) Fassara
Coordinates 43°39′29″N 10°37′06″E / 43.658°N 10.618247°E / 43.658; 10.618247
Map
History and use
Opening1943
Manager (en) Fassara United States Army Air Forces
taswirar kasar itali

Pontedera wani wurin tashin jiragen sama musamman na sojoji ne wanda ba'a tsara shi sosai ba, wanda yake a garin Pontedera a yankin Tuskani da ke a lardin Pisa.[1]

Fili ne wanda ya dace da kowanne yanayi wanda masu bada umarni na enginiyoyi su 13 suka gina a wuri mai gan-gare, tare da abubuwa masu tsauri wanda akafi sani da suna PHS ma'ana kwalta wacce aka baza a saman wurin tare da watiyi masu inchi uku na kusurwa huɗu (square). A wannan filin suna amfani da shimfiɗaɗɗan ƙarfe a matsayin wurin ajeye ababan hawa da wasu wurarai daban da ban, alokacin buƙata. Hakkannan a wannan filin ana kafa tantina a matsayin wurin zaman soji da kuma wurin ajiye kan aiki; kuma an yi wani titi da zai rinka haɗawa zuwa titin da ake da shi a filin ; wurin zuba shara ;wurin ajiye makamai; wurin ajiye makamashi; tare da wurin ajiye ruwa tsaftatacce ; da kuma ƙaramar tashar samar ta wutar lantarki.

jiragen P-47 a wani atisaye

Daga lokacin da aka gama gina filin sai aka mika ragamar shi zuwa ga runduna sojin sama ta sha-biyu (12) a ƙarshen shekarar 1944 zuwafarkon shekarar 1945 a lokacin da itali ke tsakiyar yaƙi (yaƙin duniya na biyu) wanda sukayi amfani da shi wurin tashin jiragen yaƙin su masu suna P-47 tsawa. hakannan gida ne ga jiragen jiragen da aka sani da 416 mayaƙan-dare wanda suka ɗauki mayakan Bristol daga wannan filin a 27 ga wantan mayu da kum a 13 da watan agusta duka a shekarar 1945 a yanzu filin ya haɗa da garin an Pontedera kuma ba wani abuda yarage sai wani titi guda ɗaya a wurin rukunin masana'antu na wannan garin

[1]

  1. "Maurer, Maurer. Air Force Combat Units of World War II. Maxwell AFB, Alabama: Office of Air Force History, 1983. ISBN 0-89201-092-4."